Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Fuskantar Karayar Tattalin Arziki


Tsohon Shugaban Babban bankin Amurka, Alan Greenspan ya baiyana mawuyacin halin tattalin arzikin da ake ciki a Amurka, a matsayin wata mummunar annoba dakan faru sau daya a karni, mai kwatankwaci da guguwar tekun nan ta Tsunami.

A jiya Alhamis yayi wannan bayani wajen wani zaman Majalisar Kasar, wanda ake yi domin gano musabbabin haddasa wannan bala’i, da kuma yadda za a kaucewa aukukwar irinsa nan gaba.

Yayi adawa da tsoma bakin gwamnati cikin harkokin kasuwanci, a shekaru 18 da yayi yana shugabantar baitulmalin Amurka.

Daga Fadar White House kuma wani abin ba sabun ba aka yi, lokacin da kakakin Fadar ta White House ta fito fili tace tattalin arzikin Amurka yana kan hanyar karaya.

Ba kasafai dai jami’an Fadar White House kan yi bayani a kan tattalin arziki ba, bare ma yanzu da labarin ba mai dadin fada bane.

Perino bata kalubalanci hasashen Shugaban baitulmalin Amurka, Alan Greenspan ba, inda tace yanayin da tattalin arzikin ke ciki a halin yanzu, ya sanya lallai a gaggauta dokar tallafawa tattalin arzikin, da Shugaba Bush ya sanya wa hannu.

Tun a watan Fabrairun da ya gabata dai tattalin arzikin na Amurka ya fara nuna alamun jigata, al’amarin da yasa gwamnati ta aiwatar da wani shiri na tallafawa talakawa da wasu kudi na musamman.

XS
SM
MD
LG