Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar Da Gwamna Makaho Na Farko A Amurka


A jiya Litinin aka rantsar da David Peterson a matsayin sabon Gwamnan Jihar New York, inda ya maye gurbin Eliot Spitzer, wanda ya aje mukaminsa bayan an alakanta shi da wani gungun karuwanci.

Peterson, mai shekaru 53, shine Gwamnan New York bakar fata na farko, kuma makaho. An zabe shi dan Majalisar dokokin Jihar New York a shekarar 1985. yayi kimanin watanni 14 yana rike da mukamin Mataimakin Gwammna.

Mahaifinsa Basil Peterson, shine bakar fata na farko da ya taba rike mukamin Sakataren Gwamnatin Jihar New York. Sptzer ya sauka daga kan mukaminsa, bayan jaridar New York Times ta bada rahoton cewa an gano yana mu’amala da karuwai, a lokacin da jami’an tsaro suka yi satar jin maganganunsa ta wayar tarho.

XS
SM
MD
LG