Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsarda Sabon Frime Ministan Paksitan


Shugaban kasar Pakistan Pervez Musharraf ya rantsar da sabon Prime Minista da aka zaba, abokin hamayyarsa na siyasa yayinda wasu manyan jami’an Amurka suka isa kasar domin tattaunawa da manyan shugabannin kasar. Mr Musharraf ya rantsar da Yousuf Raza Gilani,na jam’iyar Pakistan People’s Party a fadar shugaban kasa dake Islamabad yau.

Bayan daukar rantsuwa Mr. Gilani ya yi kira ga Jam’iyun siyasar kasar Pakistan su bada hadin kai wajen shawo kan matsaloli da suka addabi kasar musamman tabarbarewr tattalin arziki. Hanun agogo yana bugawa sha biyun rana,shugaba Musharraf fiska hade ya rantsarda sabon Frime Minista Yousuf Raza Gilani,wadda yayi zaman sarka na samada shekaru hudu karkashin Musharraf

Daga nan magoya bayan Frime Ministan suka fara sowa suna cewa Allah ya dade da ran Bhutto. In ba domin kisanta ba ranar 27 ga watan Disemba,watakil,tsohuwar Frime Minista Benazir Bhutto ce tayi rantsuwar kama aiki a yau.

Jam’iyarta ce ta sami gagarumar nasara a zaben da akayi cikin watan jiya.Mabi mata itace jam’iyar Frime Minista Nawaz Shariff,wacce ta hada kai da ta abokiyar hamayyarsa wajen kafa gwamnati mai raayin kin jinin Musharraf.

Jami’an Pakistan sunce manyan kusoshin Jakadancin Amurka biyu,John Negroponte, mukaddashin sakatariyar harkokin Wajen Amurka,da Richard Boucher, karamin sakatare mai kula da shiyyar kudanci da Asiya ta Tsakiya,sun tattaunawa da shugaba Musharraf na fiyeda sa’a daya da rabi. Haka kuma ance jakadun sun shirya ganawa da sabon Frime Minista.

Tunda da farko sai da suka gana da tsohon PM kuma shugaban hamayya Nawaz Shariff, wadda kusa ne a sabuwar gwamnatin hadin gwiwa. Yace ya gayawa jakadun cewa daga yanzu Musharraf ba zai ci gaba da baiwa Washington tabbacin kome a madadin Pakistan ba,domin acewar sa zamanin mulkin mutum daya ya kare."Na gaya musu a fili cewa,nace musu Musharraf mutum ne da mulkinsa ya saba tsarin mulki,haramtaccen shugaba,wadda bashi da goyon bayan al’umar Pakistan". Tsohon PM yace dukkan matakai da shawarwari da Musharraf a ya dauka cikin shekaru takwas da suka wuce, ya dauke su ne domin muradun kansa,amma daga yanzu muradun kasa Majalisa ce zata bullo dasu.

Akwai alamar za a kai ruwa rana tsakanin shugaban kasa da Majalisa gameda bangaren shariya.

XS
SM
MD
LG