Accessibility links

An Rataye Mukarraban Saddam Hussein A Iraq


Kakakin Gwamnatin Iraq Ali al-Dabbagh, ya bada tabbacin rataye kanen tsohon shugaba Saddam Hussain, Barzan Ibrahim al-Tikriti da tsohon shugaban kotun juyin juya hali, Awad Hamed al-Bandar yau da safe. Jami’an sun ce kan Barzan ya guntule lokacin da aka rataye shi, wani abin da suka ce ba a saba gani ba, suka kuma bayyana a matsayin ikon Allah.

Surukin Bazan ya maida martani a fusace a wata hira da gidan talabijin na Al-Jazeera ya yi da shi. Ya zargi yan Shi’a da kabilanci da kuma ramuwar gayya kan ’yan Sunni.

An rataye mutanen ne bayan makonni biyu da rataye Saddam, domin kisan mutane da aka yi a Dujail a wani hali na rudani. Lamarin da ya jawo suka daga da kasashen duniya.

A halin d ake ciki kuma, mataimakin shugaban kasar ta Iraq, Tariq Al-Hashimi ya soki abokan aikinsa a gwamnati saboda rataye wadannan mutane. Hashimi wanda dan Sunni ne, yace rataye mutanen da aka yi yankan baya ne ga yunkurin da sasanta sassan dake gaba da juna domin banbancin akida. Ya shaidawa wani gidan talabijin na Birtaniya, na Sky News cewa burinsa shine ganin an ceci ran Saddam da na mukarraban nasa biyu domin karfafa shigar mutanen Iraq cikin harkokin siyasar kasar.

A wata sabuwa, wani kamfanin dillancian labarai na kasar Rasha ya ruwaito ministan harkokin kasashen ketare na kasar yana cewa. Ratayar ta baya bayan nan ba zata taimaka wajen kawo zaman lafiya a Iraq ba. Moscow tace hanyar samar da tsaro a kasar kawai ita ce kungiyoyin siyasa da na addinai su tattauna da juna tare da goyon bayan kasashe da ke makwabtaka da kasar, kamar Syria da Parisa.

XS
SM
MD
LG