Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansanda A Pakistan Sun Kama Mutane Hudu Bisa Zargin Suna Da Hanu a Tada Bam A O'tel Din Marriott Cikin Watan Jiya


Rundunar ‘yan sandan Pakistan ta sami nasarar kamo mutanen nan huɗu dake da hannu wajen tada bom a babban Otel ɗin nan na Marriot dake birnin Islamabad ran 20 ga watan satumban da ya gabata.

‘Yan sandaan na tuhumar mutanen huɗu ne da laifin kisan kai, amma ’yan sandan sun ce za’a ci gaba da tsaresu domin tambayoyi har tsahon kwanaki bakwai. Mutane sama da sittin ne suka halaka a dalilin harin ƙunar baƙin waken da suka kai da motar a kori kurar da suka lafta mata boma-bomai suka afkawa Otel ɗin.

XS
SM
MD
LG