Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gasar Kacici-Kacici Ta 2008


(Wurin da za a matsa don shiga wannan gasa tana kasa, a bayan an karanta wadannan sharrudan gasa)

Masu sauraron sashen Hausa na Muryar Amurka, bana ma Allah Ya kawo mu lokacin da muke gabatar da Gasar Kacici-Kacici domin sakawa masu sauraronmu na yau da kullum. A bana, za mu bayar da kyautar akwatunan rediyo guda hudu ne: guda uku samfurin Eton E5, guda daya kuma samfurin Grundig G-1000A.

An raba wannan gasa zuwa kashi biyu: Gasar farko, tambaya ce kan wani abinda aka gabatar a cikin shirinmu na dare (karfe 9:30 agogon Nijeriya) a cikin watan Yuli. Gasa ta biyu, zata zamo kan wani abinda aka gudanar a cikin shirinmu na dare a cikin watan Agusta.

A karshen watan Agusta, za a zabi wadanda suka amsa tambayar farko daidai. Idan yawansu ya zarce biyu, to za a yi 'yar mai-rabo-ka-samu, watau zamu gayyato wani wanda ba ma'aikacin Sashen Hausa ba ne ya zabo mana takardu biyu daga cikin wadanda suka amsa tambayar daidai. Babu wanda zai ci wannan gasa sai wanda ya amsa tambayar daidai. Amma kuma a lura cewar amsa tambayar daidai, ba wai tana nufin mutum ya ci kyautar ba ne domin kuwa idan yawan wadanda suka amsa tambayar daidai ya fi yawan kyaututtukan da za a bayar, to sai a koma ga 'yar mai-rabo-ka-samu.

Haka kuma, tilas kowace amsa ta kunshi cikakken Adireshin Gidan waya da na Email na mai shiga gasar. Idan ba za a iya amsa tambayar ta wannan filin ba, to ana iya aiko mana da ita cikinw asika zuwa ga: Gasar Kacici-Kacici 2008, Sashen Hausa na Muryar Amurka, Washington DC 20237, USA.

Idan aka rubuto amsa da adireshin Email daya fiye da sau daya, to za a watsar da sauran a shigar da guda daya kawai, domin kowa ya samu damar lashe wannan gasa kamar kowa.

Za a ji karin bayani cikin shirye-shiryenmu.

A tabbatar cewa wurin da aka ce "SUNA" an rubuta cikakken suna; inda aka ce adireshin Email, shi ma a cika, inda aka ce "Wane Irin Sako" sai a rubuta Gasar kacici-Kacici 1. Idan an bayar da amsa sai a rubuta cikakken adireshin gidan waya, da lambar wayar tarho idan akwai. Allah Ya bada mai rabo sa'a!

MATSA NAN DON SHIGA GASAR

XS
SM
MD
LG