Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Tayi Watsi Da Wasu Sharuddan Tsagaita Wuta


Kungiyar Hamas tace ba zata amince da ka'idojin tsagaita wuta da Isra'ila ta gindaya ba.

Wani shuigaban Hamas dake zaman gudun hijira a Qatar, Khalit Meshaal ya gaya wa shugabannin Larabawa dake halartar wani taron koli, cewa Isra'ila ita ce ummul hgaba'isun wannan rikici, ba Hamas ba.

Ya soki lamirin Isra'ila da daura yaki da ilahirin al'ummar Falasdinawa, cikinsu har da mata da kananan yara, wadanda basu ji ba basu gani ba.

Shima da yake nasa jawabin, Shugaba Bashar al Assad, ya goyi bayan Hamas, inda ya bukaci kasashen larabawa su yanke huldar jakadanci da Isra'ila.

Shugaba Mahmud Ahmedinejad na Iran, shima ya halarci taron, wanda aka gudanar duk da adawar hukumar Falasdinawa bangaren Shugaba Mahmud Abbas, da Masar da Saudi Arebiya.

Tun da far saida Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon yayi bayanin cewa an kusa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, bayan yayi taro da su Mahmud Abbas a birnin Ramallah, na Yamma da Kogin Jordan.

XS
SM
MD
LG