Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Najeriya Sunce Yan Kasar Su Shirya Fiskantar karin Rashin Wutan Lantarki


Hukumomin Nigeria sun bada sanarwar raguwar karfin wutar lantarki da ake samu don haka zaa fuskanci yawan daukewar wuta mafi muni a kasar.

A jiya talata ce kamfanin wutar lantarki a Nigeria ya bada sanarwar cewa yawan karfin wutar lantarkin da ake samu ya ragu da Megawatss dari takwas da tamanin, wato kashi arba’in ke nan daga cikin dari. Hakan na faruwa ne saboda rashin isasshiyar iskar Gas da ake amfani da ita wajen tada injunan dake samar da karfin wutar lanatarki.

Ana samun matsalar samun gas din saboda rikicin yankin Niger Delta. Duk da kashe Dola miliyan dubu goma sha ukun da Gwamnatin Nigeria tayi domin farfado da ƙarfin wutar lantarki tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007, yanzu dai Talaka ya rungumi addu’a kawai domin samun sa’ida.


A wani labarin kuma, Gwamnatin Comoros tace sojinta sun sami nasarar kutsen da suka kaiwa tungar mayaƙan ’yan tawaye a tsibirran Anjouan, harma sun kama shugabannin ’yan tawayen uku.

Gefe guda kuma, rundunar sojin Tarayyar Afirka sun fara haɗuwa a Comoros domin shirya ɗamarar shiga tsakani a rikicin Comoros da Anjouan. Sojin Tanzaniya ne suka fara isa Moroni, babban birnin Comoros jiya talata.

XS
SM
MD
LG