Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayiministan Birtaniya yace yakamata a gabatar da kasar Iran gaban MDD


Firayiministan Birtaniya, Tony Blair yace lokaci yayi da za’a fara tunanin kai kasar Iran gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya game da shirye-shiryenta na kera makaman Nukiliya, domin ta saka mata takunkumi. Mr. Blair ya fada a yau Laraba cewa komawar kasar Iran ga shinta na nazarin sarrafa makamashin Nukiya wata alamace dake janyo damuwa sosai. Jami’an kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus, za su gana a gobe Alhamis domin tattauna akan yadda za su gabatar da kasar Iran gaban Kwamitin sulhu na MDD. Amirka da Rasha sun nuna damuwarsu game da komawa da kasar Iran ta yi kan nazarin sarrafa makamashin Nukiliya. Tunin dai Amirka da kawayenta na kasashen Turai sun zargi kasar Iran da laifin komawa aikin kere-keren makaman Nukiliya, zargin da tunin Iran ta musanta. Da jimawa kuwa tsohon shugaban kasar Iran Hashimi Rafsanjani yace wata barazanar kafa takunkumi ba za ta hana Iran gudanar da shirta na sarrafa makamashin Nukiliya ba. Hukumar hana yadon makamai masu guba, ta Duniya IAEA, ta ce kasar Iran tana sone ta sarrafa wani Mai na makashin Nukiliya takaitacce domin nazari.

XS
SM
MD
LG