Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyun Adawa A Najeriya Sun Kasa Cimma Matsaya


Jam’iyyun ANPP da AC suyi bayani a yau cewa zasu shiga zaben. Wani hadin guiwar Jam’iyyun adawa guda 18 sunyi kurarin kauracewa zaben, tare da zargin cewa Jam’iyyar PDP ta tafka magudi.

Amma masu goyon bayan jam’iyyun adawar sun baiyan tsoronsu cewa karacewa zaben ba zai haifar da komai ba, illa kara wa jam’iyyar PDP karfi, da kuma bata dama ta kara kame madafun mulki.

Jam’iyyun adawar dai basu janye zarginsu na an tafka magudai a zaben baya ba. Sakamakon zaben da ya nuna cewa Jam’iyyar PDP tana da gwamnoni a jihohi 27 daga cikin 36.

Saidai masu sa ido kan yadda aka gudanar da zaben, sunce akwai alamun rashin tsari na zaben, musamman ta fuskar isar malaman zabe rumfunansu a kan lokaci da satar akwatunan zabe da sauransu. Akwai karin bayani bayan labaran nan.

XS
SM
MD
LG