Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasuwannin Hannayen Jari Sun Fadi Wanwar


Hannayen jari a kasuwannin zuba jari na duniya, sunyi faduwar da basu taba ganin irinta ba a shekaru masu yawa, inda aka tafka asarar abin da ya kai dollar biliyan dubu biyu a rana daya kawai.

An fi samun faduwar jarukan a kasashen Turai, da kasashe masu tasowa. Dukkan kasuwannin zuba jari guda goma sha takwas na kasashen turai sun zabgo kasa, . Babbar kasuwar zuba jari ta London tayi rashin kashi tara bisa dari, faduwa mafi girma da ta taba gani cikin kimanin shekaru ashirin. Kasuwannin Rasha sunyi faduwar kashi 19 bisa dari.

Masu hannayen jari sunyi ta rige-rigen sayar da jarukansu, bayan da manyan bankunan kasashe duniya suka rika daukar matakan kare kudaden da mutane suka ajiye a bankuna, domin a tabbatar da tsaron asusun su. Saida gwamnatocin Denmark da Jamus suka dauki matakan shiga kai tsaye, domin ceto wasu bankuna da suka tasamma rugujewa.

Ta fuskar kudaden musaya kuwa, darajar Euro wanda akle amfani da shi a kasashen Turai guda goma sha biyu, ta yiwo kasa da kashi shida bisa dari, a kan Yen na Japan, faduwar da bai taba irinta ba.

Wata masaniyar harkokin tattalin arziki, Sandy Batten ta banin Morgan Chase, tace a hangenta, tattalin arzikin Amurka ya tasamma rugujewa.

XS
SM
MD
LG