Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Lauyoyi Ta Najeriya Ta Nemi Kotu Ta Baiwa Mataimakin Shugaban Kasa Shugabanci Na Wucin Gadi


Lauyoyi a Najeriya sun bukaci wata babban kotu ta mika iko a hukumance ga mataimakin shugaban kasa Goodluck Jonatahn,har sai shugaban kasa Umaru Musa ‘Yaradua ya dawo daga jinya da yake yi a ketare. Wakilan kungiyar lauyoyi ta Najeriya sun fadawa kotu jiya Alhamis cewa, shugaba ‘Yaradua ya take tsarin mulki domin bai rubuta takarda neman a mika aikinsa ga mataimakin shugaban kasa na wucin gadi yayinda bayanan,kamar yadda tsarin mulki ya tanadaba.

Ministan shariya kuma Attorney janar Michael Aondoaka, wadda yake wakiltar gwamnati,yace kotubata daikon baiwa mataimakin shugaban kasa ikon zama shugaban kasa na riko ba.

XS
SM
MD
LG