Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Robert Mugabe ya bayyana cewa gwamnatinsa ta shawo kan annobar kwalara da ta barke a kasar


Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya bayyana cewa gwamnatinsa ta shawo kan annobar kwalara da ta barke a kasar, abinda ya kai ga shugabannin kasashen yammaci yin kira da ya yi murabus.

Ya bayyana haka ne yau a jawabin da ya yi ga kasa da aka yayata ta kafofin sadarwa, jim kadan bayanda MDD ta kiyasta cewa adadin wadanda suka rasu sakamakon kamuwa da wannan cutar ya kai dari bakwai da tamanin da uku.

Mr. Mugabe yana zargin shugabannin yammaci da fakewa da annobar wajen neman su hambare gwamnatinsa. Yace yanzu da yake an shawo kan wannan cutar babu bukatar ci gaba da cecekuce. Jami'an kiwon lafiya suna ci gaba da yaki da cutar a daidai lokacin da shugaban kasar yake wannan harsashen.

Yau din ne ma Afrika ta Kudu ta bayyana kan iyakarta da Zimbabwe a matsayin mai cike da hadari sabili da wannan annobar.

XS
SM
MD
LG