Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Liberiya Zata Fara Safarar Lu'u - Lu'u


Ranar Talata Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta kara bayar da tabbacin cewa zata cika ka’idojin Majalisar Dinkin Duniya na amfani da kudin da za a samu daga cinikin lu’u lu’un, wajen gudanar da aiyukan sake ginin kasa.

Ana ganin fasa kwaurin wannan ma’adini shine daya daga cikin dalilan da suka haddasa yakin basasar da ya daidaita kasar, da ma makwabciyarta Saliyo.

A ranar Juma’ar da ta gabat, majalisar Dinkin Duniya ta dage haramcin shekaru shida da ta sanyawa fataucin lu’u lu’un Liberiya. Majalisar tace Kasar ta Liberiya ta cika ka’idojin da aka shimfida na dawo da cinikin ma’adinin, ciki har da wata ka’ida da ta baiwa kasashe ikon tantance asalin danyen lu’u lu’u kafin a sayeshi.

XS
SM
MD
LG