Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kan Mumbai Ya Halaka Akalla Mutane 175, Ciki Har Da 'Yan Kasashen Ketare


Jiga-jigan ’yan siyasar jihar Maharashatra ƙasar Indiya biyu na daga cikin waɗanda guguwar rikicin harin ta’addanci Mumbai ya rutsa dasu, domin muƙaman dasuke riƙe dasu a Gwamnati na yin ɗigirgire.

Harin ta’addancin Mumbai ya janyo asarar rayukan mutane 175 cikinsu harda ’yan ƙasar waje goma sha takwas.

Wadanda ke rike da mukamai biyu mafiya girma a Jihar da Mummbai take, da alamun suna kan hanyarsu ta yin murabus,bayan harin da aka kai kan birnin Mumbai. Babban ministan maharashtra, Vilisrao Deshmuk, ya ce a shirye yake ya ajiye aiki kan rauni da aka samu kan harkokin tsaro. Rahotannin kafofin yada labarai sun ce jihar ta sami bayanai dake gargadin ana shirin kawo hari kan Mumbai.

A wani taron manema labarai cike da hayaniya,’yan jaridu sun bukaci tabbas kan makomar ministan,abinda kawai ya gaskanta sine ya mika takardar barin aiki,yace shugaban Jam’iyyarsa CP shi yake da alhakin yanke hukunci.

Duk shawara da shugabanni suka yanke.Ina gaya muku cikin kalmomi masu saukin fahimta. Ba kwa bukatar wani karin bayani.

Haka kuma, Deshmuk ya sha suka saboda daukar dansa fitacce a silima,da kuma wani shi ma fitacce cikin masu yin silima a Bollywood na India, suka rufa masa baya a ziyarar da ya kai O’tel din Taj Mahal,yayinda ake fitarda gawarwaki daga muhallin.

Shi ma mukaddashin Ministan Deshmuk,R.R. Patil,zai yi murabus, saboda ya kira harin na Mummbai cewa “ai karin al’amari ne”. kalaman sun janyo kakkauasar suka. Daya daga cikin manyan siyasar a tarayya da harin na Mumbai ya sha da shi shine ministan harkokin cikin gidan da bashi da farin jinni. Jiya lahadi ya yimurabus.

Kiran da a kori Shivraj patil ya juma kamin harin kan Mumbai cikin makon jiya. Ya sha suka saboda rashin gamsuwa da matakan Gwmnati kan jerin hare haren boma- bomai da akai kan wasu biranen India da dama a bana.
Ministan kudi Palaniappan Chidambaram da ake mutuntawa ne zai maye gurbin Patil. Palaniappan yace zai koma ma’aikatar cikin gida wacce a karkashinta ne harkar tsaron cikin gida take,sai dai yace bai ji dadin haka ba sosai.

XS
SM
MD
LG