Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Amurka Tayi Watsi Da Kudurin Rage Kudin Yakin Iraq


Dan Jam’iyyar Democrat mai wakiltar Mazabar Wisconsin, Russ Feingold shine ya kawo kudurin rage kudin, inda yace Janye sojojin daga Iraq, zai fadada ya kuma inganta hanyoyin murkushe aiyukan ta’addanci, a kasashen duniya, kai har ma da gida Amurka.

Wannan mataki ya kawo baraka tsakanin ‘yan Jam’iyyar Democrat. Shugaban Kwamitin Aikin Soja na Majalisar, Sanata Carl Levin daga Mazabar Michigan, yace yana adawa da duk wani yunkurin yanke kudin sojojin Amurka.

Kakakin Fadar White House Tony Snow, ya yaba wa Majalisar dattawan, saboda daukar matakin, inda yace babu gudu babu ja da baya.

Amma masu goyon bayan kudurin, sunce sannu a hankali suna kara samun goyon baya. Hasali ma, Sanatocin Democrat masu neman tsaya mata takarar shugabancin kasa, wato Hilary Clinton ta Mazabar New York, da Barak Obama na Mazabar Illinois, wadanda a da ke dari-darin da gogyon bayan yanke kudin, yanzu sun fito karara sun goyi bayan kudurin.

Sauran masu kyamar yakin, sunce wannan kuduri, duk da bai kai gaci ba, yana basu kwarin guiwar cewa, wata rana zasu kai ga nasara.

XS
SM
MD
LG