Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kamfanonin Kera Motoci A Amurka, Zasu Bayyana A Gaban Kwamitin Majalisar Dokokin Amurka.


Yau Talata shugabannin kamfanonin kera motocin Amurka zasu bayyana gaban Majalisar Dokoki,domin neman tallafi ga masana'antun dake fama da matsaloli.

Shugabannin kamfanonin General Motors, da Ford da Chrysler, tare da shugaban kungiyar ma'aikata dake yiwa kamfanonin aiki duk za su bada shaida gaban kwamitin majalisar Dattijai dake nazarin matsalar masana'antun ke fuskanta.

Wakilan Democrat a Majalisar suna goyon bayan ayi amfani da dala miliyan dubu ashirin da biyar daga kudade da aka ware domin ceto bangaren kudi domin tallafawa masu kera motocin.Amma gwamnatin Bush tace kuskure ne a baiwa kamfanonin kudaden ba tare da sunyi garambawul ta yadda za su ci riba ba.

Gwamnatin ta Bush tana bada shawarar kamfanonin kera motocin su sake tsara abinda ke hanunsu ta wajen amfani da rance da aka basu a baya ta hannun Ma'aikatar makamashi.

XS
SM
MD
LG