Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhimman Bayanai Sun Yi Layar Zana A Birtaniya


Ministan Kudi na Birtaniya, yace wasu na’urori biyu dake adana bayanan kwamputa , dauke da bayanan asusun banki da haraji na kimanin mutum n miliyan 25, sun bata a Ofishin haraji na Kasar.

Minista Alistair Darling ya gayawa ‘yan Majalisar Kasar a yau Talata cewa wannan ba karamin sakaci bane daga bangaren Ofishin Tattara Haraji da Kudin Fito. Yace Hukumar ta rasa na’urorin guda biyu ne, bayan ta aike dasu ta gidan waya zuwa Ofishin Binciken Kudin Gwamnati.

Darlin yace ‘yan sanda suna kokarin samo na’urorin, koda yake har yanzu babu wata alama dake nuna cewa sun fada hannun bata gari. Da sanyin safiyar Talata, Shugaban Hukumar Tattara Harajin, Paul Gray ya sauka daga mukaminsa, saboda batan na’urorin.

Wakilan Jam’iyyar Adawa ta ‘Yan Mazan Jiya, sun soki lamirin gwamnati da sakacin jefa rabin al’ummar Birtaniya cikin hadarin fadawa hannun ‘yan damfara.

Na’urorin dai suna dauke da sunayen rukunin iyalai har miliyan bakwai, wadanda ke karbar tallafin rikon iyali. Kuma akwai cikakkun sunayensu, da lambobin inshorarsu da adireshin gidajensu da bayanan asusunsu na ajiya a banki.

XS
SM
MD
LG