Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Yana Sallama, Bush Yana Ban Kwana


A yau, ranar jajiberen rantsar da shji a matsayin Shugaban Amurka na 44, Barack Obama ya gudanar da wadansu aiyuka na jin kai, a ci gaba da hidimomin ranar tunawa da Martin Luther King Junior.

Shugaban mai jiran gado ya ziyarci wani gidan matasa marasa galihu, inda ya gaida ma'aikatan sa kai da suke taimakawa a gidan, ya kuma dauki burushi, ya shafa fenti a wani wajen da ake aikin fenti.

Daga nan sai suka wuce wani zauren wasanni na stadium a nan Washington, inda uwargidansa Michelle ta taimaka wajen rarraba kayan agaji ga dakarun Amurka.

A wani gefen kuma, Shugaban kasa mai barin gado, George Bush, yayi tattaunawar bak kwana da wasu shugabannin kasashe a yau Litinin, inda ya gode masu saboda hadin kan da suka bashi a shekaru takwas na mulkinsa.

A wannan rana wadda ita ce ta karshe a tsawon mulkinsa, Bush yayi magana da Prime Minista Vladmir Putin da Shugaba Dmitri Medvedev na Rasha, tare da Shugaban Isra'ila Shimon Peres, da Shugaba Nicholas Sarkozy na Faransa da kuma Shugabar Jamus Angela markel.

Ya ma zanta da Shugaban Brazil Luiz Inacio Da Silva, da Mikhail Saakashvili na Georgia, da Lee Myung-bak na Korea ta Kudu, da Firayim Miniostan Italiya Silvio Berlusconi, da Gordon Brown na Birtaniya da Taro Aso na Denmark da Anders Rasmussen da kuma tsohon Shugaban Kasar Mexico Vincent Fox.

Kakakin Fadar White House, Gordon Johndroe yace Shugaba Bush ya gaya wa shugabannin kasashen cewa yaji dadin aiki da su, ya kuma gode masu saboda karimcin da suka nuna masa.

XS
SM
MD
LG