Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Darfur Ya Hana Aikin Jin Kai


Aiyukan jin kai a yankin Darfur da yaki ya ragargaza, suna fuskantar mummunanan yanayin rashin tsaro. A kalla hukumomin Majalisar Dinkin Duniya 14 ne suka bayar da wata sanarwa ta hadin guiwa ranar Laraba, inda suka ce yawan hare hare, da yawan kungiyoyi masu dauke da bindigogi, da rashin takamaiman matsugunin mabukata, yana hana aiwatar da aikin jin kai yadda ya kamata.

Hukumomin suka ce a kalla mutun dubu 250 aka raba da mullansu a cikin watanni shida da suka wuce, sakamakon kone kauyukansu, ko sace kadarorinsu, ko kuma sako masu ruwan bama-bamai.

An lalata kayan amfanin gona, an karkashe dabbobin gida, an kuma yiwa matan da ba zasu kirgu ba fyade da sauran nau’o’i na azaba. Sanarwar tace akwai karin tursasa ma’aikata a yankin, gashi kuma ma’aikatan jin kai 12 aka kasahe cikin watanni shida da suka wuce. Hukumomin sun bukaci sassan dake gaba da juna da su mutunta dokokin jin kai, kuma su bada hadin kai wajen kawo zaman lafiya mai dorewa a yankin na darfur.

XS
SM
MD
LG