Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Hadakar Mawaka Ta Sa'adu Zungur Zata Cika Shekara Guda Da Kafuwa


Kungiyar hadakar mawaka da ake kira "Sa'adu Zungur Entertainment Group" tana shirin gudanar da bukukuwan cikar shekara guda da kafuwa. Wannan kungiya ta Sa'adu Zungur, tana da cibiyarta a Kanon Dabo.

Kungiyar Sa'adu Zungur ta kunshi mawaka kamar Mudassiru Kassim, Misbahu M. Ahmed, Adam M. Kirfi, Salisu Babba Hotoro, Aminu Ladan Abubakar (Aminu Ala) da kuma Maryam A. Baba (Maryam Sangandale).

A cikin tattaunawar da suka yi da filin "A Bari Ya Huce..." wasu daga cikin 'ya'yan kungiyar sun bayyana makasudin kafa ta, da manufofinta da matsayinta a yanzu da kuma irin abubawanm da ta sanya a gaba.

Mudassir Kassim, jami'in shirye-shiryen kungiyar, ya ce kungiyar tasu ta samo asali ne daga hadakar da suka ga ya dace su yi a tsakaninsu su mawaka. Manufofinsu kuwa in ji Mudassiru, sun hada da "...kare mutuncin addini...al'ada...mutuncin sana'armu da kuma yarenmu." Ya ce sun dauki sunan Sa'adu Zungur ne a saboda irin gudumawar da ya bayar wajen wake-waken fadakarwa, da siyasa da kuma farkar da jama'a ga irin 'yancin da suke da shi.

Misbahu M. Ahmed kuwa cewa yayi kungiyar ta su ta Sa'adu Zungur tana bayyana manufofinta ne ta hanyar wakoki tun da dukkan membobin kungiyar duk mawaka ne kuma da wakar aka sansu. Ya kara da cewa idan suka rungumi manufa, to su na kokarin su yada ta ne ta hanyar shirya wakoki.

Shi kuwa Salisu Babba Hotoro, yayi karin bayani da cewa a yanzu waka wata babbar kafa ce ta yada sako ga kowane irin jinsin al'umma. Ya ce sun dauki wani gagarumin shiri na yada zaman lafiya, domin a cewarsa, "...duk wani ci gaban al'umma ba zai samu ba sai an zauna lafiya." Shi ya sa a yanzu sun raba ma kawunansu fannoni dabam-dabam na zaman lafiya kowa yayi waka a kai, alal ga misali Maryam A. Baba ta yi wakar cewa Mace Ta Gari ita ce sila ta zaman lafiya, Aminu Ala yayi wakar muhimmancin ilmi ga Zaman Lafiya, Salisu Babba yayi wakar muhimmancin Soyayya ga azaman lafiya; Adam Kirfi ya ce Tarbiyya ce silar zaman lafiya, yayin da Mudassiru Kassim ya ce Shugaba Adali shi ne tushen zaman lafiya.

A lokacin da shi kuma yake tofa albarkacin bakinsa, Adam M. Kirfi ya ce daya daga cikin dalilansu na kafa wannan kungiya shi ne gudun kada a barsu a baya ganin cewa su mawaka ba su da kungiyar hadaka irin wannan. Ya ce ganin kowa yana da irin basirara da Allah Yayi masa, idan suka hada karfi wuri guda, su na iya taimakawa juna da jama'a tare da kawar da abinda ya kira "Bara-gurbi" da wake-wake na batsa a cikin wannan sana'a ta su.

Idan ana son jin kashin farko na wannan hira da 'yan Sa'adu Zungur Entertainment Group sai a mtsa rubutun dake saman wannan labari don a ji.

XS
SM
MD
LG