Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Fatattaki Tsagerun Niger Delta


Kakakin rundunar sojin, Laftanar Kanar Sagir Musa yace ‘yan bindiga sun kai hari kan wadansu kananan jiragen ruwa da masu gadin mahakar man suke, a tsibirin Bonny Island na Jihar Rivers.

Yace tsagerun sun zo wajen ne cikin wadansu kananan jiragen ruwa guda shida. Ya kara da cewa sojojin sun gwabza fada da tsagerun har saida suka fatattake su, har ma suka kwace wadansu makamai daga hannun tsagerun.

Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dauku dawainiyar wannan hari da aka kai kan ma’aikatar sarrafa danyen man fetur mafi girma a Najeriya.

Tashe tashe hankula sun tsananta a wannan yanki na Niger Delta, wanda ke kudancin Najeriya, yawanci kuma anfi kaiwa ma’aikatun hakar man fetur hare-hare, a sace ma’aikatansu, a kuma lalata injinansu.

An dai tabbatar da cewa wasu daga cikin masu kai harin, kungiyoyi ne kawai na ‘yan daba, koda yake kungiyar nan mai da’awar ‘yanto yankin Niger Delta, ta MEND, ta dauki nauyin yawancin hare-haren.

XS
SM
MD
LG