Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin NATO Sun Kashe Farar Hula A Wani Luguden Wuta


Hukumomin kasar Afghanistan sun ce an kashe farar hula tara a wani hari da kungiyar tsaro ta NATO ta kai ta sama, a ci gaba da arngamar da suke yi da ‘yan gwagwarmaya lardin arewa maso gabashin kasar.

Cikin wadanda suka mutu har da mata biyar da kananan yara uku. Hukumomi sunce NATO ta bukaci a kai harin ta sama ne lokacon da ‘yan gwagwarmayar suka yi masu dirar mikiya, da yammacin jiya lahadi. Mai magana da yawun rundunar sojhin Amurka yace ana binciken lamarin, amma dai yace bashi da bayanin wadanda suka jikkata a harin.

A can kuma gundumar Nagahar ma, jami’an Afghanistan sunce an kashe a kalla mutum tara, lokacin wata musayar wuta tsakanin sojojin Amurka da ‘yan gwagwarmaya, wadanda suka kai wani harin kunar bakin wake kan jerin gwanon motocin Amurka.

Shugaba Hamid Karzai ya bayar da umarnin a gudanar da bincike kan kashe kashe na jiya Lahadi. Jami’an Amurka sunce ba a dai san wanda yayi kisan ba, tsakanin sojion Amurka da ‘yan gwagwarmayar.

XS
SM
MD
LG