Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Janye Karbar Bakuncin Wasannin Kwallon Kafa Kofin Duniya Na matasa Kasa Da Shekaru 17, A Badi.


An fara rade raden Najeriya bazata iya daukar nauyin gudanar da wasan kwallon kafa na Duniya na matasa kasa da shekaru 17,na kofin Duniya da za ayi badi ba,bayan da Gwamnatin kasar tace bata da kudi dala milyan talatin da ake bukata domin gudanar da wasannin.

Shugaba Umaru Musa 'Yaradua ya gayawa majalisar Ministocin sa cikin makonjiya cewa baya jin karbar bakon cin wasanin cikin watann Nuwamban badi zai kara habaka wasannin a Najeriya. Ya kara da cewa yana sha'awar ganin kwamitin gudanar da wasanin ya tuntubi masu hanu da shuni wajen gudanar da shi.

Jiya Talata wata jaridar Najeriya ta buga labarin cewa Najeriya ta janye daga karbar bakuncin wasanin. Duk da haka wani jami'in kwamitin ya musanta wannan rahoto,yana cewa kwamitin bashi da masaniyar wani shirin Gwamnati na janyewa daga daukar nauyin bakuncin wasannin.

XS
SM
MD
LG