Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkawa Sunyi Zanga-Zangar Adawa Da Ziyarar Paparoma


Turkawa a birnin Ankara, sunyi zanga-zanga mafi girma da aka taba yiwa paparoma Benedict don nuna rashin amincewarsu da ziyarar da yake shirin kaiwa kasarsu.

Paparoma Benedict zai fara ziyararsa ta kwana hudu a birnin Ankaran ranar Talata, amma masu wannan zanga-zanga sunce basa marhabun da zuwan nasa. Mujahid Jafar, yana daga cikin dubun dubatar matasa da suka shiga zanga-zangar, ya kuma shaidawa Muryar Amurka cewa basa so Paparoman ya shiga kasarsu, saboda yayi amfani da kalmomi na rashin girmamawa ga Annabi Muhammadu (SAW). Abin da ya batawa Turkawan rai.

Watanni biyu da suka wuce, Paparopman ya taso da wata kurar tarzoma a kasashen musulmi, lokacin da ya ari ra’ayin wani tsohon Sarkin daular Baizantiyawa, wanda ya kwatanta tarbiyyar musulunci da takadaranci da keta.

An dai tsaurara tsaro a wajen wannan zanga-zanga, wadda jami’iyya mai akidar Addinin Musulunci ta Saadat,(wato ‘yan uwantaka) ta shirya. “Yan sanda dubu hudu tare da motoci masu sulke aka saka cikin shirin ko-ta-kwana, daga sama kuma ga jirgi mai saukar ungulu yana ta shawagi.

Wani mai Magana da yawun shugaban jam’iyyar, Mustafa Kaya, yace a kullum Turkiyya tana maraba da baki, amma Paparoman yayi abin da ba za a lamunta ba, kuma lallai ya nemi afuwa.

Yace “bama goyon bayan ziyarar domin sai ya fara da neman afuwa. Lallai ya nemi afuwa. Akwai musulmi miliyan dubu biyu a duniya. Idan dai ana so a sami kyakkyawar alaka tsakanin addinai, to lallai ko a fahimci juna, kuma lallai a mutunta juna”.

Paparoman dai yace yayi nadamar yadda wannan furuci nasa ya janyo tayar da jijiyar wuya, ya kuma ce ba wai furucin yana nuna ra’ayisa bane.

A wajen zanga-zangar dai, mata sun sanya hijabai, matasa kuma suka daura janjami a kawunansu, dauke da rubutun da yake cewa “kada kazo Paparoma”, wadansu kuma suna dauke da kyallaye dake cewa “Paparoma, yi zamanka a gida.”

Daga can Birnin Roma kuwa, Paparoman ne yayi jawabi ga wadansu maziyarta a dandalin Saint Peters, inda yai maganar ziyarar da zai kai Turkiyyan, kasar musulmi ta farko da zai taba ziyarta. Ya baiyana yadda yake girmama mutanen Turkiyya, tare da mika fatansa na aminci da kawance garesu. Ya kuma bukaci ayi masa addu’a kan wannan ziyara ta kwana hudu, ga kasr da yace tayi fice ta fuskar tsohon tarihi da kyawawan ta’adu.

XS
SM
MD
LG