Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Tawayen Assam Sun Kashe Indiyawa Sama Da Sittin


Daruruwan sojoji na sintiri a tsaunukan Assam, inda tsagerun Kungiyar ‘Yanto Assam suka kashe dimbin mutane, a wani sabon tashin hankali da ya barke ranar juma’ar da ta gabata. Wannan hari ya faru ne a jiya Lahadi, duk kuwa da tsauraran matakan tsaro da aka kafa, da kuma umarnin harbin kan mai uwa da wabi, da aka baiwa jami’an tsaro. Yawancin wadanada aka kashe din dai talakawa ne, ma’aikata daga sauran sassan India. Wadansu daga cikinsu ma suna barci a gida aka bisu aka bindige.

Daruruwan mutane ne suka cika manyan hanyoyi a yayin wata zanga-zanga dake nuna kyamar hare-haren. Yawancin ma’aikatan da ba ‘yan asalin Assam ba kuma suna ta tserewa zuwa garuruwansu, cike da kaduwa. Hukumomi dai suna ta kokarin sama masu matsugunai. Ba wannan ne lokaci na farko da waccan kungiya take kaiwa wadannan talakawa ma’aikata hari ba. Kungiyar dai taece tana yakin kwatar ‘yanci ne ga al’ummarsu, wacce ta sha bamban da sauran yankunan kasar Indiya.

‘Yna tawayen sun zargi ‘yan kabilar hindu masu rinjaye, da mamaye guraben aiki a ma’aikatun gwamnatin taraiya, ta kuma zargi gwamnatin da kin gudanar da aiyukan raya kasa a yankunansu, duk kuwa da arzikin ma’adinai da ake samu daga yankin. Wannan hari dai ya biyo bayan rugujewar wata yarjejeniyar zaman lafiya a watan Satumba, lokacin da gwamnati ta ci gaba da kai masu hare haren soji, bayan ‘yan tawayen sunce ba zasu tattauna ba sai an saki shugabanninsu da gwamnatin ta kame. Jami’an tsaron gwamnati da sunci gaba da kai hare haren a halin yanzu, inda suke farwa mafakar ‘yan tawayen.

Karamin Minista Sriprakash Jaiswal ya ziyarci yankin a jiya Lahadi, inda yayi Allah wadai da wadannan hare-hare, ya kuma ce gwamnati zata dauki matakan kare lafiyar al’umma a yankin. Shima dai Babban Minista Mai Kula da Assam, Tarun Gogoi yayi alkawarin daukar tsauraran matakan magance irin wadannan hare-hare. Saidai yace har yanzu gwamnati a shirye take da a koma kan teburin tattaunawa.

XS
SM
MD
LG