Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kuri'ar  Neman Jin Ra'ayin Jama'a Ta Nuna Obama Kan Gaba Da Abokin Hamayyar sa John McCain,Ana Sauara Mako Uku Ayi Zabe


Dan takarar shugaban Amurka na Jam'iyyar Republican,John McCain,yace zai fafata wajen maida tsarin tattalin arzikin Amurka kan gaba,a dai-dai lokacin da kuri'ar neman jin ra'ayin jama'a take nuna cewa yana baya da abokin hamayyar sa na Democrat,Barack Obama,mako uku kafin ayi zabe.

Senata McCain,ya gayawa gangamin siyasa a jihar Virginia,litinin din nan, cewa shugaban Amurka mai zuwa tilas ya dauki matakai cikin hanzari wajen magance matsalar tattalin arziki da Amurka ke fuskanta.

Shi ma Senata Obama, zai bada sanarwar shirin tallafawa Amurkawa a wannan hali na matsatsin tattalin arziki,a lokacin yakin neman zabe da zai yi nan gaba kadan a birnin Toledo dake Jihar Ohio,Jihar dake da muhimmancin gaske a takarar shugabancin Amurka tsakanin 'yan takarar biyu.

XS
SM
MD
LG