Accessibility links

Akalla Mutane 60 Suka Halaka A Abidjan, A bikin Shiga Sabuwar Shekara.

  • Aliyu Imam

Mutane suke tsaye a gefen kayayyaki na mutane da suka yi turereniya a daren jiya, a Abidjan.
Jami’ai a kasar Cote ‘d Voire sun ce a kalla mutane 60 ne suka mutu bayan da aka sami turereniya a safiyar yau Talata a Abidjan, babban birnin kasar.

Masu agajin gaggawa sunce wasu mutane 200 ne suka jikkata a wanna lamari, wanda ya faru a gundumar da ake kira Flato,wani filin wasa wajenda mutane suka taru domin kallon wasannin kayan wuta na shigar sabuwar shekara.

Tashar talbijin ta AIP a kasar ta bada labarin cewa, galibin wadanda lamarin ya rutsa da su matasa ne. Iyaye wadanda hankalinsu ya tashi sun dunguma zuwa filin wasan domin neman 'yayansu cikin gawarwaki da suke wurin.

Hukumomin kasar sun kaddamar da bincike domin tantance dalilinda ya janyo turereniyar.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG