Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Bangladesh Jerin Tsawa Sun Halaka Mutane Fiyeda 50 Cikin Kwanaki Biyu.


Ana sallar wata gawa a Bangladesh.

Wannan ya biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwariya da aka yi a duk fadin kasar.

A Bangladesh, hukumomin kasar suka ce tsawa ta halaka mutane 55 a wurare daban daban, cikin kwanaki biyu da suka wuce, al'amari da ya tsorata jama'a.

Bayan da aka tafka rana mai tsanani na kusan mako daya, sai kuma ruwan sama kamar da bakin kwariya suka afkawa gundumomi 14 da suke kasar ranar Alhamis, har tsawa ta halaka mutane 33. Sannan wasu jerin tsawan suka farwa kasar jiya jumma'a, da halaka akalla mutane 23.Haka nan wasu mutane masu yawa sun jikkata sakamakon lamarin.

Bayanai daga rundunar 'Yansanda sun ce, galibin wadanda lamarin ya rutsa da su suna aiki ne a gonaki, ko a filin Allah, yayinda musibar ta afka musu.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG