Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Bukuru Jihar Filato Ginin Makaranta Ya Hallaka Yara


Yara kanana 'yan makaranta

Wata makaranta mai ginin bene ta rushe kan 'yan makarantar ta kuma yi sanadiyar mutuwar yara da dama

Makarantar Islamiya dake garin Bukuru kusa da Jos babban birnin jihar Filato ginin benenta ya rikito kan wasu yaranta.

Yara da dama suka rasa rayukansu wasu da dama kuma sun jikata.

A cewar wasu ganao lamarin ya auku ne da yammacin jiya yayinda yaran suke kan karatun islamiya a makarantar Abu Naima cikin garin Bukuru.

Lawal Bala shugaban matasa na yankin Bukuru yace sun bada agaji wajen zakulo yaran daga baraguzan ginin.Wasu sun mutu kodayake ba'a iya samun alkaluman adadin wadanda suka mutu ba.

Wadanda suka mutu wasu an kaisu wajen iyayensu wasu kuma an kaisu asibiti. Yau za'a cigaba da neman gawarwaki saboda a san adadin wadanda suka rigamu gidan gaskiya.

Dahiru Musa Mai Turare wani shugaban al'umma a garin Bukurun ya shaidawa Muryar Amurka cewa suna rokon gwamnati ta agazawa yaran da suka jikata. Yace masu bada gudummawa sun yi kokari, wato irinsu NEMA da limaman gari duk sun bada gudummawa.

Banda wadanda iyayensu suka kwashesu akwai yara sama da talatin suna kwance a asibitin Filato da NEMA ta kaisu.

Ga rahoton Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

XS
SM
MD
LG