Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A China An Sami Karin Mutum Da Murar Tsuntsaye Ta Kashe.

Ma'aikatan kiwon lafiya a Hong Kong suke yanka kaji da ake zaton sun kamu da murar tsuntsaye.
Ma'aikatan kiwon lafiya a Hong Kong suke yanka kaji da ake zaton sun kamu da murar tsuntsaye.

Kasa da wata daya baya mutuwar da ake azawa cutar murar tsuntsaye, yau lahadi China ta sake bada labarin wani mutum daya kuma ya mutu, bayan kuma mutuwar wani mutum a Vietnam da kuma jariri a Cambodia.

Jami’ai suka ce yau lahadi ne mutum na baya bayan nan ya rasu a kudu masu yammacin lardin Guizhou, bayan an kwantar da shi a Asibiti tun ranar 6 ga wata. Mutumin dan shekaru 39 da haifuwa an ce baiyi wata cudanya da kaji ba.

A karshen watan jiya wani matukin motar kiya-kiya a lardin Guangdong, shima ya mutu sakamakon kamuwa da cutar murar tsuntsaye.

Galibi cutar tana kama mutane da suka hadu da tsuntsaye da suka kamu da cutar.

Wasu masana kimiyya suna fargabar cutar da ake kuma kira H5N1 tana iya rikida ta yadda mutane zasu iya kamuwa da cutar daga Bil-Adama dan’uwansa maimakon ta tsuntsaye, yadda ake kamuwa da cutar ahalin yanzu, kuma hakan yana iya janyo mutuwar miliyoyin mutane.

XS
SM
MD
LG