Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Puerto Rico Dubun Wasu Masu Fataucin Miyagun Kwayoyi Ta Cika


Hodar Iblis
Hodar Iblis

Hadin gwuiwar jami'an tsaron Amurka da Colombia ya yi sanadiyar fasa gungun wasu masu fataucin miyagun kwayoyi na kasa da kasa inda yanzu mutane 30 dubunsu ta cika a Puerto Rico

Jami’an tsaron Amurka da na Colombia sun fasa wani gungun masu fataucin muggan kwayoyi na kasa da kasa, suka damke mutane 14 bisa zargin safarar dubban kilo na hodar iblis ta Cocaine zuwa cikin yankin Puerto Rico.

Jami’an Amurka sun ce damke wadannan mutane da aka yi cikin makonni biyun da suka shige ya kawo adadin wadanda aka kama dangane da wannan dogon bincike zuwa 30, yayin da kuma aka kama hodar Cocaine fiye da kilo dubu biyu.

Lauyar gwamnatin tarayya ta Amurka a Puerto Rico, Rosa Emilia Rodriguez-Velez, ta fada jiya Litinin cewa, “zamu ci gaba da matakan hadin kan da hukumomi da kasashe ke dauka tare da hada karfi waje guda domin bincike da hukumta wadanda suke take dokokinmu, suke shigar da muggan kwayoyi cikin yankunanmu…”

An tuhumi mutanen da aka kama da laifin hada baki domin yin fasa kwabrin hodar iblis ta Cocaine daga Colombia zuwa Amurka ta cikin yankin Puerto Rico.

Ana iya yanke wa mutanen hukumcin daurin shekaru goma zuwa rai da rai idan har aka same su da aikata wannan laifi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG