Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A India Dubban Mutane Suka Nemi A Yiwa Matan Da Aka Yiwa Fyade Adalci


Gangamin neman a yiwa wasu 'yan mata biyu da aka yiwa fyade adalci

Duk da dokoki masu tsanani da kasar india ke dasu akan fyade har yanzu sai karuwa wannan mugun abu keyi lamarin da ya sa dubban mutane a duk fadin kasar suka yi gangamin neman a yiwa wasu 'yan mata biyu da aka yiwa fyade adalci

Dubban mutane ne suka hallara a fadin India jiya Lahadi, suna bukatar ganin an yiwa 'yan mata biyu adalci sakamakon fyade da aka yi musu, lamari da ya sa 'yan kasar suke tamabayar me yasa kare 'yan mata da mata baki daya yake zama kalubale duk da dokoki masu tsanani da ake da su.

Wannan shine taron jama'a mafi girma da yake nuna fushinsu tun bayan fyade irin wadda ake kira giwa ta fadi da aka yiwa wata daliba a babban birnin kasar ta India, lamari da ya janyo zanga zanga a duk fadin kasar.

Dauke da kwalaye a biranen New Delhi, da Mumbai, da Bengaluru, da Kolkata, masu zanga zangar sun yi kiran da a dauki mataki cikin hanzari na hukunta wadanda suka aikata laifin, a kuma gaggauata shari'ar masu bata yara kanana tareda yanke musu hukunci mai tsanani. A rataya masu irin wannan laifin," kamar yadda wasu rubuce rubuce da suke kan kwalayen suke fadi.

Cikin masu zanga zangar harda wata ma'aikaciya 'yar shekaru 37 da haifuwa Aditi Sengupta. Tace ta kai intaha. Na gaji da yadda kasan nan take wulakanta mata.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG