Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Iraqi An Hana Wasu Manyan 'Yanmajalisar Kasar Balaguro Bisa Zargin Cin Hanci


Firayim Ministan Iraqi Haidar al-Abadi
Firayim Ministan Iraqi Haidar al-Abadi

Firayim Ministan Iraq, Haider al-Abadi, ya bada umurnin a hanawa wasu manyan shugabannin majalisun dokokin kasar tafiye-tafiye a cikin kasar saboda zargin cewa su maciya hanci da karbar rashawa ne.

Ofishin Firayim Ministan din yace wannan matakin na wucingadi ne da za’a ci gaba da aiki da shi har zuwa lokacinda aka kamalla gudanarda bincike akan ‘yanmajalisar.

An dauki wannan matakin ne dai a sanadin kukan da ministan tsaro na kasar Khaled al-Obeidi ya shigar a jiya Litinin na cewa Kakakin majalisar Salim al-Jabouri da wasu wakilan majalisar sun nemi suyi mishi yankan baya don yaki basu wasu manyan kwangiloli da suka nema na gwamnati. Daman ministan tsaron ya je gaban majalisar ne inda ya karbi tambayoyinta akan zargin almundahanar da akace tana gudana a cikin ma’aikatarsa.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG