Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jahar Lagos Hukumar Kwastam Ta Kama Wasu Makamai Da Aka Shiga Da su Najeriya


Shugaban Hukumar Kwastam Reshen Tashar Ruwa Ta Tin Can A Lagos
Shugaban Hukumar Kwastam Reshen Tashar Ruwa Ta Tin Can A Lagos

Hukumar Kwastam reshen tashar jiragen ruwan Tin-Can dake Lagos, ta kama makamai da harsashi 7,500 da sauran kayayyakin sojoji da akayi kokarin shiga da su Najeriya daga Amurka ba tare da izini ba.

Shugaban hukumar Kwastam na tashar Tin-Can Alhaji Bashar Muhammad, yace an kama manyan bindigogi biyu da harsasai 7,500 sai kuma sulke da hular kwano da takalma, wanda duk wani ‘dan Najeriya yayi kokarin shigar da kayan.

Yanzu haka dai hukumar Kwastam sun mika mutumin da suka kama ga hukumar tsaro ta DSS domin gunadar da bincike a kansa.

A cewar Alhaji Bashar Muhammad, anyi kokarin shigowa da kayayyakin ne ta hanyar amfani da kwantainar da gwamnati ta baiwa duk wani ‘dan Najeriyar da ya zauna a wata kasa a kalla watanni tara damar shigowa da kayansa ba tare da ya biyawa kayansa haraji ba.

Domin karin bayani saurari tattaunawar da shugaban Kwastam Alhaji Bashar Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:52 0:00

XS
SM
MD
LG