Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Koma Gidan Jiya Game da Komawar Gwamna Danbaba Ofis


Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai mai fama da rashin lafiya bayan hatsarin jirgin saman a Adamawa a shekarar 2012

Cece-ku-ce da cacar baki sun kara barkewa a jahar Taraba game da lafiya, ko rashin lafiyar gwamna Danbaba Suntai

An mayar da gwamna Danbaba Suntai gida a Jalingo jahar Taraba daga wani asibitin birnin London. Gwamnan ya koma gida ne a daidai lokacin da Majalisar zartaswar jahar ta bukaci kafa wani kwamitin kwararru na mutum biyar ya binciki lafiyar gwamnan wanda ke jinya tun shekarar dubu biyu da goma sha biyu bayan hatsarin da yayi a jahar Adamawa a cikin karamin jirgin saman shi da yake tukawa da kan shi a lokacin.

Da safiyar nan ta Litinin an sanya garin Jalingo cikin shirin ko ta kwana inda 'yan sanda suka yi ta shawagi cikin motocin su bisa la'akari da alamun da mukarraban gwamna Danbaba suka nuna cewa zai shiga ofis.

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:21 0:00
Shiga Kai Tsaye


A daidai wannan lokaci ne kuma cece kuce da cacar baki dajifan juna da kalamai suka dada kunno kai a jahar tsakanin masu ra'ayin cewa Gwamna Danbaba Suntai ya warke an sallame shi daga asibiti kuma zai koma aiki, da kuma masu ra'ayin cewa ba ki suka yi gwamnan ya koma ofishin shi ba, amma da farko kwararru su yi binciken tabbatar da cewa gwamnan ya na da koshin lafiyar iya ci gaba da mulkin jahar. Kamar dai yadda za ku ji bayani a cikin rahoton da Ibrahim Abdulaziz ya aiko daga Jalingo, babban birnin jahar taraba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG