Kundin tsarin mulkin kasar Niger ya tanadi daukan wannan mataki, bisa abubuwan da demokaradiyya tayi tanadi domin walwalar talakawa.
Mai sharaa Ali Shina Kogeni Amadu shine sakataren janar na hukumar ta CND ASH.
Yace kudiri na 12 na dokar data kafa wannan hukumar ta kasa mai kare hakkin Dan Adam ita ta bada wannan umurni. Tace idan aka zabo kwamishina, to kafin ya soma aikin sa ya kamata a rantsad dashi a gaban majilisa. Hakan yana da muhimmaci sabo da ana janyo hankalin su domin suyi aiki da adalci har wa yau suyi aiki cikin sirri, domin cikin aikin da suke yi, zasu ji zasu gani abubuwa abinda bai kamata su bayyana shi ba’’
Kwamishinonin dake da waadin shekaru 4 amintattu ne daga majilisar dokokin kasa da kungiyoyi daban-daban, da suka hada da alkalai, da lauyoyi da kungiyoyin kare hakin mata, dana kwadago sai wakilan kungiyoyin manoma da makiyaya.
Metro Musa na wakiltan kungiyoyin Lauyoyi na kasa.
Ga Sule Mummuni Barma da Karin bayani.
Facebook Forum