Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jamhuriyar Nijar Gwamnati Zata Dauki Matakin Inganta Noman Rani


Kimanin garuruwa 869 ne suka fuskanci fari cikin garuruwa 3,378 a jahar Damagaram, abin da yasa gwamnati daukan matakin shirin inganta noman rani, hakan ya biyo bayan wani rangadin da karamin Minista na ma'aikatar noma da kiwo yayi a jahar Damagaram.

Karamin Minista Mallam Ahaman Moussa, ya bayyana sakamakon abinci sakamakon yawan abincin da aka samu a damunar bana, a wani zagayen gani da ido a Damagaram. Ministan yace damuna ta fara a kwanaki goma na karshen watan Mayu a garuruwa 712 na jihar Damagaram, yayin da kuma mutanen yankin suka yi shuka a watan Yuni, an kuma fuskanci lalacewar shukoki a wasu gundumomi.

Dangane da al’amuran kiwo kuwa kimanin tan Miliyan uku da Dubu 632 aka samu, alhali ana bukatar tan Miliyan shida da Dubu 54 don amfanin dabbobi Miliyan 3 da 500 a tsawon watanni takwas, abin da ya haddasa gibin abincin dabbobin har tan sama da Miliyan biyu.

Ministan yace gwamnati zata inganta noman rani a matsayin mataki na maye gurbin karancin abincin da aka samu a kasar.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:04 0:00

XS
SM
MD
LG