Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jamhuriyar Nijar Jam'iyyar MNSD Ta Gaji da Adawa


Shugaban Nijar Issoufou Mahammadou

A jamhuriyar Nijar jam'iyyar MNSD mai adawa ta gaji da adawan yanzu kuma ta mika kai bori ya hau saboda ta amince ta karbi tayin shiga gwamnatin hadin kai da shugaban kasar ya yi mata.

Bisa ga alamu babbar jam'iyyar adawa ta jamhuriyar Nijar ta mika kai bori ya hau saboda ta amince ta shiga gwamnatin hadaka da shugaba Issoufou ya yi mata tayi makon jiya.

Bayan sun kwashe tsawon Asabar da ta gabata suna muhawara da kace-nace da cecekuce, masu ra'ayin a dama dasu a gwamnati sun samu rinjaye.

Dan majalisar dokokin kasa Murtala Alhaji Mamuda shi ya dauki sanarwar karshen taron. Yace matsalar tattalin arziki da matsalar tsaro suka sa 'yan jam'iyyar suka amince da tayin gwamnati. Cikin mambobi dari da arba'in da takwas hudu ne kawai basu yadda ba. Saboda haka zasu shiga su taka tasu rawar a gwamnatin.

Sakataren watsa labaran jam'iyyar na kasa baki daya Tambura Issoufou dake adawa da shawarar shiga gwamnati yace hujjojin da uwar jam'iyyar ta bayar domin shiga gwamnatin hadaka da Issoufou Mahammadou ke shirin kafawa ba masu gamsarwa ba ne. Yace me ya sauya zani da har zasu shiga gwamnain. A ganinsa babu wata hujja illa talaucin zuciya da na kudi.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG