Wannan halin nema yasa a bana ba’a gudanar da hawan gaisuwar sallah da akan yi a fadar manyan sarakunan jihohin biyu.
Wasu Magidanta sun bayyana halin da suka yi wannan bikin Sallar, kamar yadda wanna n magidanci ke cewa.
‘’To Sallar Alhamdulillahi gaskiya ba laifi duk da yake mun tashi munyi salar cikin ruwa duk da yanayi da ake ciki kuma ka san yanayin na aljihu ba zamu ce kome ba, gashi yanayi na damuna amma tunda dai anyi sallar cikin koshin lafiya alhamdulillahi’’
Kamar magidanta suma yara kanana ba’a barsu a baya ba a shagulgulan sallar inda suka nuna farin cikinsu.
Koda yake yayin da wasu ke kokawa, wasu yan majalisu sun tuna da jama’ar su a wannan karon. Dan Majalisa Sulieman Alkali shike wakiltar mazabar Yola ta arewa a majalisar dokokin jihar Adamawa ya bada kayakin tallafi mazabar sa da suka hada da shanu, da buhun shinkafa buhu 80 da sifageti kwali 72.
Ga wakilin sashen Hausa Ibrahim Abduazeez da Karin bayani 2’11
Facebook Forum