Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jihar Bauchi Wata Mata Ta Kashe Jaririn Kishiyarta


 Matar da ta kashe jaririn kishiyarta
Matar da ta kashe jaririn kishiyarta

Wata da ta ce an yi mata auren dole ta kashe jaririn kishiyarta daga bisani kuma ta yi nadama tana neman gafara.

Kakakin rundunar 'yansandan jihar Bauchi DSP Kamal Datti Abubakar shi ya tabbatar da kashe jaririn da wata mata ta yi tare da yiwa manema labarai karin bayani.

A cewarsa ranar 19 ga watan da ya gabata ne a wani kauye dake cikin karamar hukumar Alkaleri ne a gidan wani Abdullahi ita matar ta shiga dakin uwargidan ta dauki jaririnta ta bashi guba.

An kai yaron gidan magani dake kauyan amma rai yayi halinsa. Yace ita matar da ta aikata danyen, aikin an kamata tana hannunsu.

Matar ta amsa laifinta da kanta ba tare da wani matsi ba. Yanzu 'yansandan na shirin gurfanar da ita gaban kotu domin a yi mata hukumci.

A zantawa da manema labarai Malama Yindatu Abdullahi Ori ta amsa laifinta ta ce auren dole aka yi mata. Tace babu zancen kishi akan batun. Tana mai cewa tsautsayi ya sa ta aikata mummunan aikin. Ta roki Allah ya yafe mata.

Malama Yindatu tace babu soyayya tsakaninta da mijinta kuma idan ta fadawa mahaifinta sai ya koreta amma mijin wanda ya je aikin hajji ya yi alkawarin bata takardar saki idan ya dawo.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG