Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jihar Filato Shugabannin Fulani da Berom Sun Kira Al'ummominsu Su Rungumi Zaman Lafiya


Gwamnan Jihar Filato Mr. Simon Lalon

Sabo da gujewa sake aukuwar rigingimun da suka auku tsakanin Berom da Fulani a jihar Filato, shugabanninsu sun kira al'ummominsu da su rungumi zaman lafiya tare da gindiyawa kansu wasu sharuda domin a cigaba da zama tare cikin lumana.

Shugabannin al'ummomin Fulani da Berom a kananan hukumomin Bassa da Barikin Ladi a jihar Filato sun kira al'ummomin yankinsu da su rungumi zaman lafiya da juna.

Kiran ya biyo bayan barnata dukiyoyi a wasu kananan hukumomin jihar ta Filato.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen karamar hukumar Bassa Umar Dakari yana mai cewa ba sa fatan sake ganin irin rikicin da ya auku shekarun baya ba.

Yace kimanin shekaru 15 noma da kiwo duk suka zama haram. Amma yanzu an samu zaman lafiya saboda haka suna son kowa ya kula da kayansa kuma duk yaron da yayi kiwo a gonakin mutane kungiyar Fulani ba zata lamunta dashi ba. Za'a hukumtasu. Yace duk wanda aka yi masa barna kada ya dauki doka a hannunsa ya shaidawa Miyetti Allah zata magance.

Shugaban kungiyar raya yankin Ropp a Barikin Ladi Joseph Chollom Jack yace suna fatan ganin dangantakarsu da Fulani ta koma kamar yadda take lokacin da suke yara. Ya kira Berom da Fulani da Hausawa da ma sauran kabilu su rungumi juna a zauna lafiya.

Ga rahoton Zainab Babaji da cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Facebook Forum

Bidiyo

Mijin Aljana A Kano: Shin Dama Aljanu Na Da ATM’ Na Kudi?
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG