Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jihar Neja Batun Katin Zabe da Sauran Rina a Kaba


INEC
INEC

A yau alhamis ne hukumar zabe ta Najeriya, zata kamala aikin yin rajistar zabe a jihar Neja hukumar zaben dai tace a jiya laraba ne ya kamata a rufe aikin amma a bisa la’akari da yawan jama’ar da basu samu ba yasa aka kara lokaci zuwa yau alhamis.

Duk da wannan Karin lokaci jama’a na korafi da nuna rashin gamsuwa da yadda aikin ya gudana, tuni dai shuwagabanin kungiyoyin jama’a, suka koka tare da yin kira ga hukumar zaben data canja matsayi.

Dangane da wannan Gwamna jihar Dr. Mua’azu Babangida Aliyu, ya bukaci hukumar zabe wato “ INEC” da ta bullo da wata hanya da duk wanda aka yiwa rajista ko bai samu kati na dindindin ba yayi zabe

Hukumar zaben dai tace a yanzu haka mutane miliyan daya ne suka karbe katin zaben na dindindin a jihar Neja, daga cikin mutane miliyan daya da rabi da aka yiwa rajista a baya, sauran mutane dari biyar kuma zasu karbe katin su ne a ofisoshin hukumar dake kananan hukumomi.

Katin Zabe - 2'44"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

XS
SM
MD
LG