Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jihar Niger Delta, Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sace Turawa Hudu


Tsagerun 'yan Niger Delta

Wasu ‘yan bindiga a jihar Niger Delta sun sace turawa hudu ‘yan asalin kasar Birtaniya

A jihar Niger Delta dake kudu-maso-kudancin Najeriya, wasu ‘yan bindiga da ba’a tantance ba sun sace turawan Ingila su hudu.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin ta bakin kakakinta, Andrew Onyemeka.

Yace ‘yan wata kungiya da ake kira “Karowel” ne suka sace mutanen, wadanda likitoci ne dake aikin jinkai na kiwon lafiya kyauta.

Rundunar ‘yan sandan ta ce tana shirye ta hada karfi da karfe da wasu jami’an tsaro domin ceto mutanen da aka sace.

Kawo yanzu rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cafke wasu mutane dangane da lamarin.

Mutanen da aka sace likitoci ne kuma ‘yan aikin mishan ne da suka kwashe shekaru fiye da goma suna aiki a kauyuka daban daban na yankin.

Ga Lamido Abubakar Sokoto da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG