Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kare Muradun Fulani Ta Nemi Gwamnati Ta Kafa Dokar Ta Baci A Jahar Taraba.


Sojojin Najeriya.

Wannan kiran ya biyo bayan rikici tsakanin Fulani da kabilar Mambilla a tsaunin dake jahar.

Gwamnatin tarayya zata tura Karin jami’an tsaro zuwa yankin Mambilla dake jahar Taraba, inda rikici na baya bayan nan ya janyo hasarar rayuka da dukiya mai yawwa.

Kakaki a fadar shugaban Najeriya Mallam Garba Shehu, shine ya bayyana wannan mataki a hira da yayi da wakiliyar Sashen Hausa Madina Dauda. Garba Shehu yace wannan shine mataki na farko da gwamnati zata dauka kamin ma ta fara binciken gano wanene yake da laifi.

Wata kungiya mai kare muradun Fulani a yankin da ake kira Pastoral Resolve wacce ta kira taron manema labarai ta nemi gwamnatin tarayya ta kafa dokar ta baci a jahar taraban domin gwamnatocin jahar daga matakin karamar hukuma zuwa jaha basu da niyyar kashe wannan wuta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG