Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kamaru Boko Haram Ta Halaka Mutane 4 Ta Raunata 10.


Sojojin kamaru.

Al'amarin ya auky ne a yanki da ake kira Mora a jahar Arewa Mai nisa.

Gwamnatin kamaru zata dauki matakai na binciko ‘yan boko Haram tsakanin ‘yan gudun hijira daga Najeriya da suka sami mafaka a kasar.

Mai baiwa Ministan tsaro shawara ta fuskar yada labarai Lawwali Jika ne ya bayyana haka, bayan da wani dan kunar bakin wake ya kai hari a wani kauye da ake kira Omaka dake yankin Mora, ya halaka mutane 4, da jikkata mutane 10, a jahar Arewa mai nisa.

Harin da aka kai a farkon makon nan, ya tada hankalin jama’a, yasa gwamnatin take shirin bi gida-gida domin tabbatar da wadanda suka sami mafaka tsakanin ‘yan gudun hijira daga Najeriya ba ‘yan Boko Haram bane.

Tuni dai aka garzaya da wadanda suka jikkatan zuwa asibiti dake Mora inda suke karbar jinya.

Jami’an tsaron kasar sun bayyanawa wakilin Sashen Hausa Awwal Garba cewa, an sami nasarar tarwatsa yunkurin da wani maharin na daban yaso ya kai a barikin sojojin kasar dake kan iyakar kasar da Najeriya.

Sai dai hukumomi basu yi Karin bayani kan hali da maharin na barikin sojoji yake ciki ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:51 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG