Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kano 'Yan Najeriya Sun Yi Tsokaci kan Dawowar Buhari


Dawowar Shugaba Mohammadu Buhari daga Birnin London
Dawowar Shugaba Mohammadu Buhari daga Birnin London

Mutanen Kano da suka yi furuci sun yi tsokaci akan yajin aikin malaman jami'a da sha'anin tattalin arziki da tabarbarewar tsaro da rabuwar kawuna tsakanin bangarorin gwamnati da majalisa da na shari'a.

Wadda ta fara magana tace abun da ya fi mahimmanci shi ne shugaban ya huta ya murmure da kyau kana ya maida hankali kan matsalolin jami'o'i domin malamansu dake yajin aiki yanzu su koma.

Shi ko Yusuf Lawal Babale fata ya yi shugaban kasa ya maida hankali akan harkar tsaro da tattalin arziki tare da hada kawunan jama'a.

Baicin 'yan Najeriya da suka yi tsokaci kungiyoyi masu zaman kansu na ci gaba da bayyana ra'ayinsu dangane da alkiblar da ya kamata shugaban ya kalla a yanzu.

Kwamred Nura Iro Ma'aji jami'i ne a kungiyar dake bibiyar ayyukan majalisun dokoki da shugabanci nagari yana mai cewa sun yi magana ya kamata shugaban kasa ya fitar da wata matsaya akan fadi in fada da bangarorin kasar suke ta yi. Haka kuma bayan ya bar kasar harkokin ta'addanci sun sake farfadowa. Haka ma sace sacen mutane a kasar ke yaduwa.

Ma'aji ya jaddada mahimmancin dangartaka tsakanin bangarorin zartaswa da na majalisa da shari'a. Bai kamata shugaba ya bar rabuwar kawuna tsakaninsu ta samu tushe lokacin da yake mulki ba, injishi. Ya kamata a zauna a gayawa juna gaskiya.

Yanzu malaman jami'o'i sun kwashe mako guda suna yajin aikin "sai baba ta gani". Farfasa Mahmud Lawal shugaban kungiyar malaman reshen shiyar arewa maso yammacin kasar yana cewa suna farin cikin dawowar shugaban kasa.

A kungiyarsu ta malaman jami'o'i suna kallon gwamnati a matsayin abu mai cigaba kullum kuma duk wani abu da aka faroshi duk wanda ya zo mulki zai dora a kai sai a ci gaba.

Yace sun yi yarjejeniya da gwamnatin baya. Sun yi zaton gwamnatin da ta zo zata aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma amma hakan bai samu ba har suka shiga yajin aikin.

Suna fatan dawowar shugaban wani abu mai mahimmanci zai faru domin su koma bakin aikinsu dalibai kuma su koma karatu.

Ga rahoton Mahmud Kwari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG