Jami’an sun ce wani soja ya sami rauni lokacin da dan kunar bakin waken ya tunkaro wurin akan babur ya kuma tada nakiyoyin, a wani wurin da sojojin suke bincike motoci kusa da birni Gao yau jumma’a.
Dakarun faransa masu marawa dakarun Mali baya, suna fuskantar karin turjiya daga yan tawayen islamar a arewacin Mali a yan kwanakin nan, bayan da dakarun suka kwato iko a yankin a watan da ya gabata.