Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Shugaba Buhari Ya Ziyarci Maiduguri


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

Tun lokacin da ya zama shugaban kasa sai wannan karon ne Shugaba Buhari ya kai ziyara Maiduguri jihar Borno kuma yankin arewa maso gabashin kasar

Tun lokacin da ya zama shugaban kasa sai wannan karon ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci Maiduguri a jihar Borno cikin yankin Arewa maso Gabashin kasar tare da samun rakiyar manyan hafsoshinsa.

Shugaban ya je Maiduguri ne domin gudanar da bikin samun ‘yancin kan kasar na 57 ne tare da sojojin da suke yaki da kungiyar Boko Haram.

Binkin dai an gudanar da shi ne cikin barikin Maimalari inda shugaban ya gana da sojojin da suka samu raunuka lokacin da suke gwabzawa da ‘yan Boko Haram.

Gwamnan Borno Kashim Shettima da Shehun Borno duk su ma sun halarci bikin.

A cikin jawabin da yayi Shugaba Buhari ya godewa gwamnan Borno saboda karfin halin da ya nuna. Kuma shugaban na Nigeria ya tabbatarwa sojoji cewa gwamnati zata ba su duk kayan aiki da kudaden da suke bukata don cika aikinsu.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:41 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG