Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karshen Wannan Shekarar Amurka Za Ta Maida Ofishin Jakadancinta Birnin Qudus


Mataimakin Shugaban Amurka, Mike Pence, da Benjamin Netanyahu, Firayim Ministan Israila
Mataimakin Shugaban Amurka, Mike Pence, da Benjamin Netanyahu, Firayim Ministan Israila

A yayin ziyarar da ya kai Gabas ta Tsakiya, Mataimakin Shugaban Amurka, Mike Pence ya ce nan da karshen wannan shekarar kasarsa za ta maida ofishin jakadancinta zuwa Birnin Qudus, furucin da ya harzuka Larabawa dake cikin majalisar dokokin Israila kaucewa jawabinsa amma kuma Netanyahu ya yi na'am dashi

A yau Litinin Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence yace Amurka zata maida ofishin jakadancin ta zuwa birnin Qudus a karshen shekarar nan ta 2018.

Shugaban Amurka Donald Trump ya kauce manufofin Amurka na shekaru da shekaru, da ya ce Birnin Qudus ne babban birnin Isra’ila kuma ya sa a kaurad da ofishin jakadancin Amurka daga Tel-aviv, wanda yanzu shi ne babban birnin Israila, zuwa birnin na Qudus. Amman Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson, ya ce tashin nasu zai dauki lokaci mai tsawo.

Netanyahu ya godewa Trump da Pence akan abinda ya kira “ kalamai da za su shiga tarihi”, kuma ya ce dangantaka tsakanin Amurka da Israila tana nan kuma bata taba karfi ba kamar yanzu.

Shawarar da shugaba Trump ya yanke akan birnin Qudus ta janyo zazzafar suka daga shugabannin Palasdinu, ciki harda shugaba Mahmoud Abbas, wanda ya ce Amurka ba za ta iya taka wata rawa ba akan yunkurin wanzar da zaman lafiya a yankin.

Larabawa 'yan majalisar dokokin Isra'ila sun ce zasu kauracewa jawabin da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence zai gabatar. Mr. Nethanyahu ya soki wannan matsaya da wakilan Larabawa suka dauka, a zaman majalisar ministocin Isra'ila da aka yi jiya Lahadi.

Ahalinda ake ciki kuma, wasu 'yan majalisar dattijan Amurka 'yan Republican masu sassaucin ra'ayi sun bayyana kwarin gwuiwar yiwuwar samun maslaha da za ta kai ga sake bude gwamnatin Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG